Tsaya ka karanta, wannan manhajar an kirkireshi ne domin taimakawa yan uwa almajirai masu aikin makaranta.
Ana karanta fatiha kafa 364 sai kuma a karanta Qulhuwa Kafa 364 kullum insha Allahu in dai mutum ya rike wannan lazimin wallahi sai Allah ya azirta shi kuma ya hore masa duk abunda yake nema Alfarmar Annabi muhammadu
idan kanason ka tashi cikin dare a dai dai ko wanne lokaci kake so kuma kana tunanin zaka iya zarcewa baka tashi ba to ka jarraba wannan sirrin duk lokacin da kake so insha Allahu a lokacin zaka tashi, Ana karanta fatiha kafa 41 lokacin da mutum zai kwanta bacci bayan ka karanta sai kace (Aqsamtu billahi alaikum ya kuddamu hazihissuratul shariyfat an tuquzuniy bilwaqti (sai ka fadi lokacin) bihaqqiha alaikum wafadaliha ladaikum barakallahu fikum wa alaikum) insha allahu in har kayi haka zaka ga ikon Allah
Wannan saboda Amfanin gona ne da kuma bishiyoyi masu yayan na lambu, yanda ake aikin shine ana karanta fatiha kafa 364 a ruwa mai tsarki sai a yayyafa akan gona ko kuma bishiyoyi insha Allahu in har ana yin hakan to insha Allahu za'a samu amfani mai Albarka in Allah ya yarda
Wanda yake son dukiyarshi yai ta karuwa koda yaushe to ya jarraba wannan sirrin insha Allahu zai ga abun mamaki, ana rubuta ayar nan اهدنا الصرط المستقيم kafa 4444 sai kafa 313 يا غنى يا رزاق a takarda ayi laya a ajje a inda ake neman Arziki insha Allahu zaa bamu labari
Ga masunta masu kamun kifi ana samun kwanan jan karfe sai a rubuta masa wannan ayar (صرط الذين انعمت عليهم) a farkon sa,ar zuhal ranar asabar kenan sai ka saka wannan kwanon a ruwa insha Allahu kifaye zasuyi cincirindon zuwa gun wannan kwanon wanda da hannunka ma xaka kamasu insha Allahu.
Ga mai wata bukata wajen ubangiji to ya jarraba wannan sirrin insha Allahu zai yi godiya, duk wanda yakaran fatiha zuwa iyaka naabudu wa iyaka nastain sannan sai ya karanta qulhuwa sannan sai yace (Allahuma ajma'a baynani wa bayna hajatiy kama jami,at bayna isma,ika wa siffatika ya zaljalali wal ikram ya bidi,ussamawati wal ard ya hayyu ya qayyum) kafa uku sannan sai ya karasar da fatihar zuwa karshe, to haka zai yi tayi har fatiha kafa 313 insha Allahu zai ga biyan bukata.
Wannan maganin mantuwa ne da kuma karin hazaqa, ana rubuta fatiha akan kwarya ko akan wani kwano sai a bawa yaro ko kai sai ka lashe, insha Allahu zaka samu kaifin tunani kuma maganin mantuwa ne, ana wannan aikin tsawon kwana 7
Wannan duk wanda akayi masa sata kuma yana son a dawo masa da kayanshi to ya jarraba wannan sirrin, ana karanta fatiha kafa 28 a ko wacce kusurwa na inda akai maka satar gabas 28 yamna 28 kudu 28 arewa 28 bayan ka gama karantawa sai kace (Ya Rijalullahi ujlibu, Ya Auliya'allahi Araba,ina warduw li sarqan minni barakallahu fikum) insha Allahu zaa dawo maka da kayanka bi izinillahi ta,ala
Domin yin sasanci tsakanin mutum biyu ko kuma neman biyan wata bukata agun wani musamman babban mutum ko wata masarautar, ana karanta fatiha kafa 1000 amma a duk kafa daya idan kaxo kan wannan ayar (اياك نعبد واياك نستعين) sai ka karanta qulhuwa sannan sai wannan azimar (Allahumma kama jami,at baina asma,ika wa siffatika ajma'a baini wa baina (sai ka fadi sunan wanda kakeso ku samu dai daito ko budurwar da kake so ko wanda kakeson wani abun a wurinshi mata ma suna iyayin wannan aikin) bil muhabbati wal muwaddat wal shafaqatidda,ima Allati la imfisama laha ila yaumal qiyamati ya hayyu ya qayyum ya badi,ussamawati wal ardi ya zaljalali wal ikram) sai ka karasar da fatihar haka zakai tayi har sai kayi fatiha 1000 bayan ka gana fatihar gaba daya sai kace, tawakkalu billahi ya raihan bihaqqi sayyadil asfar alaika bima bina tu,umir bihi wa huwal ahraqul qalbi wa ihsha,i wa fuw,adu (sunanka ala sunanshi) bihaqqi sai ka sake karanta fatihar har karshe.