Tsaya ka karanta, wannan manhajar an kirkireshi ne domin taimakawa yan uwa almajirai masu aikin makaranta.
Ku taimaka ku danna abunda akace ku danna ta wannan hanyar ce kadai zaku iya taimakawa masu kirkirar wannan app din domin su daurashi a playstore don ganin sauran yan uwa sun amfana.
Muna fara komai da sunan ubangiji mahalicci wanda shine Al auwalu wal Akiru, cikin ikonsa da huwacewar shi, Allah ya nufe ni da fassara wannan littafin mai suna SHAMSUL MA'ARIF ALKUBRAH, na daya daga cikin manyan malamai a fanni asararu da sauran fanni, tsira da aminci su tabbata a gun masoyin mu annabi Muhammad (S.A.W) shi da ahlinsa da kuma sahabban sa Tabbas na tsinci kaina cikin farin ciki mara misaltuwa kuma ina kara godewa Allah bisa wannan ni'imar da yayi mun, Ina rokon Allah daya sanya wannan littafin ya amfani Alumar musulmi na duniya baki daya Wannan littafin mun sadaukar dashi ga malaman mu da iyayen mu wayanda sukai mana tarbiya a wannan fannin, wayanda sune fitilar mu, fatan ladan yakai kabarin su. Abubuwan dake cikin littafin: 1 - Harfofi da yanda ake ta'ammuli dasu cikin sirrukansu da kuma masu yi musu hidima 2 - Yadda ake basdi da taksir da yadda ake aiki cikin lokuta da kwanaki 3 - Hukunce Hukuncen Manziloli guda 28 4 - Hukunce Hukuncen burujai guda 12 da abubuwan da suke nunawa 5 - Tsakure daga cikin sirrukan bismillah Wayan nan sune abubuwan da littafi na farko ya kunsa
Cikin sirrukansu da kuma masu yi musu hidima Shiriya da dacewa duka na Allah ne, hakika an kasa neman dacewa gida biyu: Dacewa a duniya da kuma Lahira, kuma ko wannen su suma an kasasu bisa lissafin ko ince hisabin abunda mutun yayi niya akan shi, hakika mutane dayawa sunyi maganganu da bayanai akan abunda ya shafi lokoci, da matsayarsu akan kaukabai da riyadodi ¹ da kuma ayyukan da suka shafi dalasimai tun kamun samuwar wannan littafin, hakika wannan ilimi ne mai fadin gaske wanda halittu suke bukata da narkewa acikinsa, Manya manyan masu hikima sunyi maganganu dayawa acikin sa, kuma mutane dayawa sun samu dacewa da wayan nan maganganun nasu, to wannan abunda zan fada maka zai amfanar da kai anan duniya da kuma lahira